1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi Kongo matasyin Shugabar Kungiyar Taraiyarv Afrika

January 24, 2006
https://p.dw.com/p/BvAu

Babban taron kungiyar kasashen Afrika dake gudana a birnin Khartoum na kasar Sudan,ya zabi kasar Kongo ta zamo sabuwar shugabar kungiyar ta AU,bayan adawa mai karfi da Sudan ta samu game da karbar shugabancin kungiyar,saboda dalilan take hakkin bil adama da ake ganin zai bata sunan kungiyar.

Karkashin wata yarjejeniya da aka cimma a yau,kasar Sudan zata karbi shugabancin kungiyar daga hannu kasarKongo bayan shekara guda.

Daya daga cikin manyan kungiyoyin yan tawaye na Sudan kuma,SLA a yau tace zata ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin Sudan bayan rashin samun nasarar nata.

A jiya ne dai kungiyoyin yan tawayen suka yi barazanar janyewa daga taron Abuja na wanzar da zaman lafiya a Sudan muddin dai an zabi Sudan din a matasyin shugabar kungiyar ta AU.