An zaɓi wata ′yar Najeriya a matsayin shugabar OPEC | Labarai | DW | 27.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zaɓi wata 'yar Najeriya a matsayin shugabar OPEC

Ministan harkokin man fetir ta Najeriya Diezani Alison Madueke ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar ta masu arzikin man fetir a duniya.

Ministocin waɗanda ke taro a Vienna sun zaɓi Diezani Alison Madueke a wannan muƙami, wacce za ta fara aikin jagorancin ƙungiyar a ranar ɗaya ga watan Janairun da ke tafe.

Ministocin dai sun yanke shawarar cewar ba za su rage addadin ɗanye man fetir ɗin da ake haƙowa ba a cikin ƙasashen na ƙungiyar a kowace rana. A wani yunƙuri na magance dambarwar da ta kuno kai ta faɗuwar frashin man fetir ɗin a bisa kasuwannin duniya.