An zaɓi saban shugaban ƙungiyar gamayyar Afirka | Labarai | DW | 27.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zaɓi saban shugaban ƙungiyar gamayyar Afirka

Shugabanin ƙasashen Afirka sun naɗa Firaministan Ethiopiya Hailemariam Desalegn a matsayin saban shugaban Kungiyar Gamayyar Afirka

Ethiopian Prime Minster Hailemariam Desalegn (L) speaks during a meeting with his Somali counterpart Hassan Sheikh Mohamud (R- nicht im Bild - Anm. Bildredaktion) in Addis Ababa on November 28, 2012. Hailemariam reiterated Ethiopia?s commitment to keeping its troops in Somalia until African Union forces take over Ethiopian strongholds, but did not provide a timeline. Ethiopia sent troops and tanks into Somalia in November 2011 to support AU and Somali troops fighting Shebab extremists. They have since captured key towns from the Islamist militants, including Baidoa and Beledweyne. AFP PHOTO/JENNY VAUGHAN. (Photo credit should read JENNY VAUGHAN/AFP/Getty Images)

Hailemariam Desalegn

An naɗa Firaministan Ethiopiya Hailemariam Desalegn a matsayin sabon shugaban ƙungiyar gamayar Afirka wato AU . Kenan zai gaji shugaba Thomas Boni Yayi na ƙasar Benin bayan da aka zaɓe shi domin jan wannan ragamar a Adiss Ababa babban birnin ƙasarsa.

Daya daga cikin batutuwan da kungiyar zata taɓo yayin taron ta na cikon 20 shine rikicin ƙasar Mali Komitin Sulhu na ƙungiyar ta AU a jiya Asabar ya ba da sanarwar cewa nan ba da jimawa ba dakarunta za su iya ɗaukar nauyin yaƙin da ake yi a ƙasar , Komitin ya kuma ya ba shugaba shugaban Diocounda Traore na Mali tabbacin ba shi goyon baya. To amma kuma an yi kira gareshi da ya gaggauta shirya gudanar da zaɓe a cikin walawala.

Daya daga mahimman ƙalubalen da ke gaban saban shugaban AU shine rikicin kasar Mali.

A halin da ake ciki dai,sojojin Faransa da takwarorinsu na ƙasar Mali sun ƙwace birnin Gao mai tazarar kilomita 1200 da Bamako babban birnin ƙasar daga hannun 'yan tawaye masu kishin Islama. Firaministan Faransa Jean Marc Ayrault ya ce yana da imanin cewa dakarun ƙasarsa za su je kusa da birnin Timbuktu nan ba da jimawa na . Shi dai birnin na Timbuktu dake a hamadar Sahara yanki ne da Majalisar ɗinkin Duniya ta keɓe a matsayin ɗaya daga cikin wuraren tarihi a duniya. Su dai 'yan kishin Islama bayan da suka ƙwace iko da arewacin Mali a watan Afrilun shekarar 2012 sun lalata tsarkakun wurare na tarihi , Kamar dai yadda suka alƙawuranta a halin yanzu ƙasashen yammacin Afirka sun ce za su tura sojoji 6000 zuwa ƙasarta Mali. A ɗaya hannu kuma Faransa ta tura sojoji 2500.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi