An zaɓi El Baradei ya zama Firaminstan Masar | Labarai | DW | 06.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zaɓi El Baradei ya zama Firaminstan Masar

Shugaban ƙasar Masar na riƙo zai rantsar da tsohon jami'in Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya a matsayin Firaministan Masar a wani yunƙuri na daidaita lamuran ƙasar

Pro-reform leader and Nobel peace laureate Mohamed El-Baradei, center, wears an Egyptian flag draped on his shoulders as he is surrounded by protesters during his arrival for Friday prayers in Tahrir Square in Cairo, Egypt, Friday, Nov. 25, 2011. Tens of thousands of protesters chanting, Leave, leave! are rapidly filling up Cairo's Tahrir Square in what promises to be a massive demonstration to force Egypt's ruling military council to yield power. The Friday rally is dubbed by organizers as The Last Chance Million-Man Protest, and comes one day after the military offered an apology for the killing of nearly 40 protesters in clashes on side streets near Tahrir over the last week. (Foto:Bela Szandelszky/AP/dapd)

Mohamed El Baradei

An zaɓi madugun 'yan adawan Masar Mohammed Elbaradei a matsayin sabon Firaministan ƙasar, Ƙungiyar Tamarod wacce ke bayan boren da ya kifar da jagorancin shugaba Mohammed Mursi ce ta bayyana hakan bayan da ta gana da shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya.

Wata majiyar sojin ƙasar ta bayyanawa kamfanin dillancin labarun Faransa AFP cewa idan an jima za a rantsar da tsohon jami'in hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wato wuni uku ke nan bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mursi

Haka nan ma kamfanin dillancin labaran ƙasar na MENA ya bayyana cewa Elbaradei, yana tattaunawa da sabon shugaba Adly Mansour, wanda ake sa ran zai rantsar da shi da yammacin yau.

To sai dai Jamiyyar 'yan uwa musulmi ta ce ba za ta amince a baiwa Elbaradei wannan muƙami ba, kuma har wa yau, magoya bayan Mursi na cigaba da bayyana fushinsu, inda suka ce suna nan suna marawa Mursi baya duk yadda aka kasance kamar yadda wannan mai zanga-zangar ya bayyana:

"A wajen mu Mursi ne shugaban ƙasa, kuma ba zai sauka ba, kuma mu zamu cigaba da zanga-zanga, ba zamu yardamu ba da kai bori ya hau ba"

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas