An zaɓi Abdullahi Gul a matsayin sabon shugaban kasar Turkiya | Siyasa | DW | 28.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An zaɓi Abdullahi Gul a matsayin sabon shugaban kasar Turkiya

Sabon shugaban Turkiya Abdullahi Gul da Uwar gidan sa Hayrunisa Gul

Sabon shugaban Turkiya Abdullahi Gul da Uwar gidan sa Hayrunisa Gul

A yayin bikin rantsuwar wanda shugaban rundunar sojin ƙasar Turkiyan janar Yasar Buyukyanit da kuma yan adawa suka ƙaurace sabon shugaban ƙasa Abdullahi Gul ya yi alƙawarin haƙƙin yan Adam da yancin faɗin albarkacin baki, bugu da ƙari yace ba zai nuna banbanci a tsakanin alúmar ƙasar ba ta kowace fuska.

Da yake jawabi ga Majalisar dokoki, Abdullahi Gul yace zai kasance wakili na dukkan alúmar ƙasar. Yace Turkiya ƙasa ce mai bin tafarkin dimokradiya wadda kuma ta kebanta daga harkokin addini tare kuma da ɗabbaƙa aƙidar gaskiya da adalci da walwalar jamaá, yace waɗannan sune ginshikan kundin tsarin mulkin ƙasar mu a saboda haka ya kamata mu rike su, mu kuma yi aiki tukuru domin kare su da martaba su.

A zaɓen da yan Majalisun dokokin suka kaɗa Abdullahi Gul ya sami adadin ƙuriú 339 inda ya doke abokan takarar sa Sabahattin Cakmakoglu wanda ya sami ƙuriú 70 da kuma Huseyin Tayfur Icli wanda ya sami ƙuriú 13 kacal.

Zaɓen dai shine karo na uku da aka kaɗa, inda a zagaye biyu na farko, Abdullahi Gul bai sami rinjayen kashi biyu bisa uku da ake buƙata ba. A wannan karon na uku yar tazara kawai ake buƙata ta ƙuriú 276 daga cikin adadin ƙuriú 550 na wakilan Majalisar dokokin.

A daren ranar Talatar nan ce Abdullahi Gul zai karɓi ragamar mulki daga shugaba mai barin gado Ahmet Necdet sezer. Tun dai bayan Abdullahi Gul ya baiyana burin sa na son zama shugaban ƙasa, aka shiga sa toka sa katsi tsakanin sa da yan adawa saboda kasancewar sa cikin wata ƙungiya ta musulmi a baya, sannan kuma suna adawa da cewa Matar sa ta yin lulluɓi. A dai ƙasar Turkiya, an haramta wa mata maáikatan gwamnati da dalibai yan makaranta yin lulluɓi ko kuma hijabi.

Yan ba ruwan mu da addini na fargabar cewa idan jamíyar AKP ta karbe ragamar iko na gwamnati dana shugaban ƙasa, to babu makawa tana iya sauya tsarin da ƙasar ke bi na tsame addini daga harkokin gwamnati.

A yanzu zaben da aka yiwa Abdullahi GUl ta kawo ƙarshen dambarwar siyasa da halin rashin tabbas da ƙasar ta faɗa a ciki a yan watannin baya lokacin da ya baiyana aniyar tsayawa takara, inda a wancan lokaci rundunar sojin ƙasar ta fito fili ta baiyana cewa zata yi dukkan abin da ga ya zama wajabi domin kare tafarkin ƙasar na babu ruwan ta da addini.

Manazarta da dama na ganin wannan mataki na rundunar sojin, ita ce ta sanya P/M Recep Tayyip Erdogan kiran gudanar da zaɓe gabanin waádi.

A yanzu yayin da ake cigaba da maida martani a game da zaɓen, shugabani daga sassa daban daban na aikewa da sakon taya murna ga Abdullahi Gul. Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya baiyana zaɓen Abdullahi Gul da cewa zai ƙarfafa ƙoƙarin ƙasar Turkiya na shiga ƙungiyar tarayyar turai. Shi kuwa kakakin maáikatar harkokin wajen Amurka Tom Casey cewa yayi suna maraba da cigaban da aka samu na dimokradiya a ƙasar Turkiya.