An zaɓi mace ta farko a shugabancin Koriya ta kudu
December 20, 2012A ƙasar Koriya ta kudu, karo na farko an zaɓi mace a matsayin shugabar ƙasa, Geun-Hye Park yar tsohon shugaban ƙasar Koriya ta kudu a zamanin mulkin soji, mahaifin na ta Park Chung-Hee a tsawon mulkinsa ya maida hankali ne bisa inganta tattalin arzikin ƙasar da kuma kare ta daga barazanar maƙobciyarsu kana abokiyar gaba wato Koriya ta arewa.
A jawabin bayan nasarar zaɓe da ta yi wa yan ƙasar, Park ta fito a fili ta bayyana cewa babban abinda za ta sa a gaba shine batun tsaro, inda ta ce harba makaman roka da Koriya ta arewa ta yi makwannin da suka gabata, wata babbar barazanace da ba za gyale ba. Don haka ta shaida wa yan ƙasar cewa "zan cika alƙawari da na yi muku na ƙarfafa tsaron ƙasar mu da kuma faɗaɗa matakan difalmasiyya"
A lokacin yaƙin neman zaɓen ta Geun-Hye Park, ta nisanta kanta da tsarin shugaba mai barin gado, wanda ya yanke duk matakan bai wa Koriya ta arewa tallafin jinƙai. A wani ɓangaren nuna manufofinta kan yankin Asiya, Park ta jaddada cewa za ta maida hankali wajen inganta tsaro a gabashin Asiya, inda yanzu haka ake taƙaddama tsakanin ƙasashen Koriya ta kudu, Japan da China bisa mallakar wasu tsibirai.
Hong Hyun-Il dake cibiyar nazarin al'amuran yau da kullum a gabashin Asiya, yace sanin halayen matar da kuma matsayin jam'iyarta, za a samu sauyi bisa dangantakarsu da Koriya ta arewa, koda yake amma abune mai yuwa ta kasance shugabar farko da za ta sasanta da Koriya ta arewa.
Kawo yanzu dai ƙasar China wanda itace ƙasa ɗaya tilo a yankin Asiya mai ɗasawa da Koriya ta arewa, ta taya sabuwar shugabar koriya ta arewa murna. A safiyar yau Park ta kai ziyara kan kabarin mahaifinta Park Chung-Hee stohon shugaban mulkin soja, kana daga bisani ta kai ziyara kan kabarin wani babban abokin adawan mahaifin na ta, inda ta yi alƙawarin ɗinke ɓarakar da aka samu tsakanin ɓangarorin biyu na tsawon shekaru 50.
A dai-dai lokacin da batun maƙobciyasu Koriya ta arewa da ma batutwan da suka shafi yankin gabashin Asiya suka kasance na gaba a hulɗar ta na harkokin waje, amma abu na farko da shugaba Park za ta sa a gaba shine matsalolin cikin gida, inda yanzu haka taɓarɓarewar tattalin arzikin duniya ya shafi fitar da haja ƙasashen waje. Koriya ta kudu tattalin arzikin ta ya fara tafiyar hawainiya, kana ana ƙara damuwa bisa kuɗin shiga aljihun gwamnati, ga kuma ƙalubalen rashin aikin yi wanda ƙasar ke fama da shi.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu