An yi zanga-zanga ƙin manufofin shugaba Hugo Chavez | Labarai | DW | 20.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi zanga-zanga ƙin manufofin shugaba Hugo Chavez

Dubun dubatan mutane sun gudanar da zanga-zanga a Caracas babban birnin kasar Venezula don nuna adawa da shirin shugaba Hugo Chavez na rufe wata tashar telebijin mai zaman kanta. Tashar da ake kira RCTV ta kulla kawance da ´yan adawa. Shugaba Chavez na zargin tashar da nuna goyon baya da wani yunkurin yi masa juyin mulki da bai yi nasara ba a shekara ta 2002. Shugaban na shirin maye gurbin tashar da wata tashar telebijin ta gwamnati. Masu zanga-zanga na ganin wannan shiri a matsayin babban koma baya ga demukiradiyya.