An yi wa ′yan wasan Super Eagles ruwan kuɗi | Siyasa | DW | 01.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An yi wa 'yan wasan Super Eagles ruwan kuɗi

Ko wane ɗan wasan Super Eagles ya samu tukuncin dalar Amirka dubu 30, kana an yi musu wani babban alƙawari in suka lashe wasansu na gaba

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF, ta cika alƙawarinta inda ko wane ɗan wasan Super Eagles ya tashi da kyautar kuɗi dallar Amurka dubu 30 a yayin da aka riɓa na mai koyar da wasu Stephen

Keshi, ya tashi da dallar Amurka dubu 60,bayan sun tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofi nahiyar Afirka da ake bugawa a ƙasar Afirka ta kudu.

Haka zalika 'yan wasan na Super Eagles, za su samu ƙarin dallar Amurka dubu 20 ko wannensu idan sun yi nasara akan 'yan wasan Elephants na ƙasar Cote d' Ivoire, a yayin da in sun ci kofin, zasu samu ladar dala dubu 30 ko wannen su.

A yayin da 'yan wasan Super Eagles na Nijeriya ke shirin fuskantar The Elephants, 'yan wasan

Ma'abuta wasan ƙwallon ƙafa a Najeriya sun baiyana ra'ayoyinsu game da wannan ruwan kuɗi da aka yi wa 'yan wasan Super Eagles.

Bayan wasa tsakanin Mali da Afirka ta Kudu da kuma Ghana da ka Verde a wannan Asabar.

Ranar Lahadi shine karo tsakanin Najeriya da Cote d`Ivoire,sai kuma Burkina Faso da Togo.

Tuni dai kasashe takwas suka koma gida wato Aljeriya, Tunisiya da Moroko, sauran sun haɗa da

Jamhuriyyar Nijar, kongo, da mai riƙe da kofi Zambiya da kuma Ethiopiya.

Mawallafi: Ado Abdullahi Hazzad
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin