An yi wa Hissene Habre daurin rai da rai | Labarai | DW | 30.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wa Hissene Habre daurin rai da rai

An yi wa Hissene Habre tsohon shugaban kasar Chadi daurin rai da rai bisa samunsa da laifi na cin zarafin al'umma da azabtar da su da kuma fyade lokacin da yake rike da madafun ikon.

Kotu ta samu tsohon shugakar kasar Chadi Hissene Habre da laifuka lokacin da ya mulki kasar, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Kotun da ke zama a birnin Dakar fadar gwamnatin kasar Senegal ta samu Habre da laifukan da suka hada da cin zarafin dan Adam da gana wa mutane azaba gami da laifukan cin zarafin mata.

Shugaban kotun Gberdao Gustave Kam dan kasar Burkina Faso ya karanta hukuncin da aka yanke wa tsohon shugaban kasar ta Chadi bayan sauraron shaidu da wadanda aka azabtar lokacin mulkin na Habre tare da hallaka kimanin mutane 40,000. Shi dai Hissene Habre ya dauki madafun ikon Chadi daga shekarar 1982 zuwa 1990, inda ya yi mulkin kama karya na tsawon shekaru takwas.