An yi wa Angela Merkel allurar AstraZeneca | Labarai | DW | 16.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wa Angela Merkel allurar AstraZeneca

Shugabar gwamnatin Jamaus Angela Merkel ta yi allurar rigakafin corona ta AstraZeneca a ci gaba da rigakafin cutar covid-19 da ake yi a kasar baki daya. 

An yi wa shugabar allurar ce a wata cibiyar rigakafin a birnin Berlin.

A wani sakon twitter da mai magana da yawun shugabar gwamnatin Steffan Seibert ya wallafa yace Merkel mai shekaru 66 da haihuwa ta baiyana gamsuwa da yi mata rigakafin ta kuma gode wa jami'an dake wannan aikin da kuma dukkan wadanda aka yi musu rigakafin.

A baya bayan nan ne dai hukumomin na Jamus suka bada shawarar yin allurar ta AstraZeneca ga mutanen da shekarunsu na haihuwa ya kama daga 60 zuwa sama.