An yi tir da harin Kenya | Labarai | DW | 03.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi tir da harin Kenya

Harin kan wata jami'a a kasar Kenya ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 150


Jama'a a garin Garissa na kasar Kenya na ci gaba da neman 'yan uwa da hari kan jami'a ya ritsa da su a birnin da ke yankin arewa maso gabashin kasar. An tabbatar da mutuwar kusan mutane 150, lokacin da maharan na kungiyar al-Shebaab ta kasar Somaliya suka kai harin.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce gwamnati tana kara karfafa tsaro domin tunkarar hare-haren 'yan bindiga.

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya yi tir da farmaki na kasar ta Kenya da ya kai ga mutuwar kusan mutane 150, abin da ya kira da aikin rashin hankali mai muni.