An yi mummunan hadarin jirgin kasa a Spain | Labarai | DW | 25.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi mummunan hadarin jirgin kasa a Spain

Wani hadarin jirgin kasa da ya auku a arewa maso yammacin kasar Spain ya yi sanadiyyar rasuwar fasinjoji 77 yayin da wasu sama da dari suka jikkata.

epa03800010 General view of the train accident of a train travelling from Madrid to Ferrol which was derailed close to Santiago de Compostela, Galicia, Spain on 24 July 2013. No details of fatalities or injuries have been made availble by the train operatives. EPA/OSCAR CORRAL

Zugunglück in Spanien

Masu aiko da rahotanni dai sun ce tarago hudu na jirgin sun goce daga layin dogon lokacin da yake kokarin shan wata kwana lamarin da ya sanya mazauna yankin da hadarin ya auku jin kara mai karfin gaske tare da fitar hayaki. Tuni dai gwamnatin yankin na arewa maso yammacin kasar ta Spain, da hadarin ya auku ta yi kira ga jama'a su bada gudumawar jini domin amfani da shi ga wadanda suka tsira da rayukansu a hadarin. Tuni dai ofishin Firaministan kasar ya bada sanarwar cewar Firaministan zai ziyarci inda hadarin ya auku domin gane wa idonsa halin da ake ciki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal