An yi macin nuna adawa da taron kungiyar G8 a brinin Rostock | Labarai | DW | 02.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi macin nuna adawa da taron kungiyar G8 a brinin Rostock

Rahotanni sun ce ana cikin kwanciyar hankali a birnin Rostock na arewacin Jamus bayan da masu adawa da shirin hadakar manufofin tattalin arzikin duniya sun fara wata zanga-zanga don nuna kyama ga taron kolin kungiyar G8 da zai gudana a Heiligendamma cikin makon gobe. Masu shirya zanga-zangar sun sa rai mutane sama da dubu 100 zasu shiga cikin macin na yau don nuna adawa da manufofin kasashe masu arziki, to amma ´yan sanda sun ce mutane kimanin dubu 30 ne suka shiga cikin jerin gwanon. An girke ´yan sanda dubu 13 a birnin na Rostock don tabbatar da macin ya tafi cikin lumana. A ranakun 6 zuwa 8 ga watannan na yuni shugabannin kasashen kungiyar ta G8 zasu yi taron koli a garin na Heiligendamm dake kusa da Rostock.