An yi kira ga ′yan kasar Kenya da su kai zuciya nesa | Siyasa | DW | 10.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An yi kira ga 'yan kasar Kenya da su kai zuciya nesa

Masu sa ido a zabe na kasashen waje sun yi kira ga 'yan kasar Kenya da su kai zukata nesa tare da kauce wa rikici, wanda tuni ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutune.

Biyo bayan rikici sakamakon zabe da aka gudanar a kasar Kenya wanda sakamakon da aka fara samu a halin yanzu ke nuni da cewa shugban kasar Uhuru Kenyatta ya kama hanyar nasara don yin tazarce, masu sanya ido na kasashen waje sun yi kira ga 'yan kasar da su kai zukata nesa tare da kauce wa rikici, wanda tuni ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutune.

An dai fara samun tashin hankali a wasu sassan kasar ta Kenya lokacin da hukumar zabe ta fara fitar da sakamakon wucin gadi, sakamakon da babban mai hamaya da shugaba Kenyatta a zaben wato Raila Odinga ya yi watsi da shi yana mai zargin cewa an tafka magudi ta hanyar yin kutse a na'urorin tattara sakamakon zabe, zargin da hukumar zaben ta musanta. Sai dai ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin da Odinga ya yi. Shi dai jagoran 'yan adawar ya yi takara a zaben shekara ta 2007, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 1000 sakamakon rikici da ya biyo sanar da sakamakon zaben.

Kenia Wahlen Thabo Mbeki und John Kerry Wahlbeobachter (Getty Images/AFP/T. Karumba)

Thabo Mbeki da John Kerry da ke sa ido a zaben kasar Kenya

Tsohon sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry, wanda na daga cikin masu sanya ido a zaben ya yi kira ga 'yan takara da jam'iyyun siyasar kasar da su bi hanyoyin da doka ta tanadar wajen nuna korafe-korafen dangane da sakamakon zaben. Ya kara da cewa ya yi amanna hukumar zaben kasar tana da sahihan hanyoyi da za ta bayyana irin sahihancin zaben da ta shirya wa 'yan kasar. Galibin masu sanya ido a zaben basu bayyana samun wasu matsaloli na azo a gani ba. A halin da ake ciki suna masu kira ga al-umma da su guji daukar zaben a matsayin abin a mutu ko a yi rai.

Shugabar tawagar masu sanya ido ta kungiyar Tarayyar Turai Marietje Schaake ta yi karin tana mai cewa.

''Ina ga hanya daya da za a mai da martani ga tashin hankali shi ne yin Allah wadai da shi. Hakki ne a kan kowa da ya zauna lafiya tare da mutunta 'yancin kowa na kada kuri'arsa da ma cigaba da zama lafiya bayan zaben.''

Shi ma a nashi bangaren shugaban tawagar sa ido na kungiyar Tarayyar Afirka kuma tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya ce sun gamsu da zaben.

''Ina ga za mu iya cewa kamar yadda muka ga farin zaben har zuwa tattara sakamakon zuwa hukumar zabe duk sun cika ka'idar da ake nema wajen mulkin dimokuradiyya."

Izuwa yanzu ba a san ko yaushe hukumar zaben za ta fidda sakamakon karshe na zaben ba, abin da take da damar mako guda kafin ta yi.

Sauti da bidiyo akan labarin