An yi kira da a kawo karshen boren da ake yiwa sojin MDD a Kodivuwa | Labarai | DW | 20.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da a kawo karshen boren da ake yiwa sojin MDD a Kodivuwa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi kira da nan take a kawo karshen boren da ake yiwa dakarun wanzar da zaman lafiyar majalisar a Kodivuwa wato Ivory Coast. Kwamitin sulhun yayi barazanar sanya takunkumi akan duk masu yiwa shirin samar da zaman lafiyar kasar da ke yankin yammacin Afirka zagon kasa. Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kira ga sassan da abin ya shafa da su yi aiki tukuru don yin sulhu tare da samar da zaman lafiya a tsakaninsu. Bayan an shafe kwanaki hudu ana zanga-zangar nuna kyamar MDD a kasar ta Ivory Coast, yanzu kura ta fara lafawa. Shugaba Laurent Gbagbo yayi kira ga magoya bayansa dake tayar da kayar baya da su kwantar da hankullansu.