An yi kira da a kara yawan sojojin Amirka a Iraki da Afghanistan | Labarai | DW | 15.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira da a kara yawan sojojin Amirka a Iraki da Afghanistan

Hafsan sojin kasa na Amirka Janar Peter Schoomaker ya yi kira da a kara yawan dakarun kasar a kasashen Iraqi da Afghanistan. A lokacin da yake magana a gaban wani kwamitin kwararru na majalisar dokoki a birnin Washington janar din ya ce idan ba´a yi haka ba to ba za´a iya gudanar da aikin da aka sa a gaba ba. Janar din ya nuna bukatar karin yawan sojoji dubu 6 zuwa dubu 7 a kowace shekara. A kuma can Iraqi an sako day awa daga cikin mutanen da wasu ´yan bindiga dadi suka sace jiya a tsakiyar birnin Bagadaza.