An yi kakkausar suka kan Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 14.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kakkausar suka kan Koriya ta Arewa

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka ga mahukuntan Koriya ta Arewa bayan da kasar ta yi gwajin wani makami mai linzami a karshen makon da ya gabata.

Kwamitin har wa yau ya shawarci mambobinsa da su dauki karin matakai wajen tabbatar da cewar takunkumin da aka kakabawa kasar na aiki yadda ya kamata sai dai bai yi karin haske ba kan irin matakan da za a dauka. Wannan dai na zuwa bayan da a jiya Litinin shugaban Amirka Donald Trump wanda kasarsa ke zaman doya da manja da Koriya ta Arewa ya bayyana a wani taron manema labarai cewar Pyongyang matsala ce babba ga duniya wadda a cewarsa za su magance ta amma kuma bai fadi irin hanyoyin da za su bi wajen yin hakan ba.