An yi jana′izar Ziad Abou Eïn na Falasdinu | Labarai | DW | 11.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi jana'izar Ziad Abou Eïn na Falasdinu

Dubban Falasdinawa ne suka hallara a wannan Alhamis din a birnin Ramalla, domin halartar jana'izar Ziad Abou Eïn, wanda ya rasu sakamakon dauki ba dadi da sojojin Isra'ila.

Hukumomi da sauran al'ummar Falasdinawa ne suka isa a cibiyar gwamnatin ta Falasdinu domin mika ta'aziyar su a gaban gawar marigayin wanda tsofon mataimakin ministan kasar ne da akasari ake kiran sa da sunan minista kuma daya daga cikin shika-shikan jam'iyyar Fatah.

Dubban jama'ar sun yi rakiyar gawar marigayin har ya zuwa makabarta mafi kusa da inda aka yi jana'izar sa. Tuni dai Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar, yayin da makarantu da shaguna suka kasance a rufe.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu