An yi jana′izar Kiristocin da aka kashe a wasu tagwayen hare-hare a Masar | Labarai | DW | 10.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi jana'izar Kiristocin da aka kashe a wasu tagwayen hare-hare a Masar

Akalla mutane 44 aka kashe a hare-haren ta'addancin da aka kai kan Kiristocin da ke zama tsiraru a kasar ta Masar a wasu birane biyu.

Masarawa mabiya addinin Kirista a wannan Litinin sun yi jana'izar 'yan uwansu, kwana guda bayan halaka akalla mutane 44 a wasu tagwayen hare-haren bam na kunar bakin wake da aka kai kan wasu majami'u biyu a wasu birane biyu na kasar lokacin bikin Palm Sunday daya daga cikin bukukuwan gabatowar bikin Easter.

Mata sun yi ta kuka lokacin da aka kai akwatunan daukar gawa a cocin Mar Amina da ke a birnin Askandariyya da ke gabar teku. Malaman cocin Kifdawa da masu makoki rike da furanni sun shiga cikin jerin masu jana'izar a cocin.

Akalla mutane 17 aka kashe a majami'ar St. Mark da ke a birnin na Askandariyya da ke zama cibiyar tarihi ta addinin Kirista a Masar. Sannan akalla mutane 27 suka mutu a daya harin da aka kai a majami'ar St. Geirge da ke a birnin Tanta.

Shugaban Masar Abdel-Fatah el-Sissi ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar a daidai lokacin kungiyar ta'adda ta IS ke karkata hare-harenta kan farar hula musamman ma Kiristoci da ke zama tsiraru a Masar.