An yi gumurzu tsakanin sojin Isra′ila da Falasdinawa | Labarai | DW | 11.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi gumurzu tsakanin sojin Isra'ila da Falasdinawa

Hatsaniya ta kaure tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra'ila a lokacin da daruruwar mutane ke zanga-zangar nuna goyon baya ga 'yan uwansu da ke yajin cin abinci a gidajen yarin Isra'ila.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na bangaren Faladinawa sun samu munanan raunuka bayan da sojojin suka yi maratanin kariya da harsasan roba. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ke maraba da shiga tsakaninn kasashen biyu don sake tattaunar sulhuntasu. A baya-bayannan shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana yunkurinsa na ganin ya kawo karshen rashin jituwa tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

A tun watan watan Afirilu da ta gabata daruruwan Falasdinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila, suka sanar da fara yajin cin abinci bisa rashin kulawa a gidajen kaso. To sai dai Isra'ila ta ce gidajen yarin kasar na cika dukkanin ka'idoji da sharuda.