An yi garkuwa da wani dan Amirka a Nijar | Labarai | DW | 27.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da wani dan Amirka a Nijar

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da sace wani dan Amrika mai aikin mishan a garin Masallata mai nisan kilomita 400 da gabashin birnin Yamai.

Da yake magana da manema labarai Ibrahim Abba Lelé kantoman jihar Konni mai makwabtaka da Najeriya, ya ce mutanen da ba a san ko su waye ba sun sace mutumin wanda ya jima a yankin yana rayuwa da iyalinsa a wata gona da ke wajen kauyen na Masallata, sai dai ba a yi wani karin haske kan inda masu garkuwa da shi suka dosa ba.

A cikin watan Oktoban 2016 wasu ‘yan bindiga sun yi sace wani dan Amirka mai aikin jin kai Jeffery Woodke a garin Abalak, daga bisani suka garzaya da shi zuwa kasar Mali, sai dai a shekarar 2019 shugaban kasar Mouhamadou Issoufou ya tabbatar da cewa mutumin na na a raye.

A cikin watan Agustan da ya gabata ma dai kungiyar IS ta dauki alhakin kisan wasu Faransawa shida a wani wurin yawon bude ido na garin Koure mai tazarar kilomita 60 daga birnin Yamai.