An yi garkuwa da turawa a Najeriya | Labarai | DW | 18.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi garkuwa da turawa a Najeriya

Rahotani da ke fitowa daga Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu turawan Britaniya hudu a jahar Delta dake a yankin Naija Delta na Kudancin kasar.

Kakakin 'yan sanda na jahar Delta Andrew Aniamaka ya tabbatar da labarin sace turawan inda ya ce wasu 'yan bindiga biyar ne suka yi awon gaba da su daga wani kauye a yayin da suke aikin kulawa da mutane  a yankin, ya kuma kara da cewa ba a ji duriyar 'yan bindigan ba kan neman kundin fansa ya zuwa lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi.