1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Garkuwa da mutane 30

Yusuf Bala Nayaya
January 16, 2019

Kimanin mutane 30 ne ake zargin 'yan awaren Kamaru sun yi garkuwa da su a yankin da ke magana da harshen Turancin Ingilishi na yammacin kasar, kamar yadda wasu rahotanni na cikin gida a Kamaru suka nunar.

https://p.dw.com/p/3BeFf
Präsidentschaftswahl in Kamerun Sicherheitskräfte
Hoto: DW/F. Muvunyi

Wata majiya ta kusa da gwamnati ta bayyana cewa mutanen an yi garkuwa da su ne a kan hanyarsu, tsakanin Buea da Kumba da ke yankin Kudu maso Yammaci. Haka kuma wata kungiya mai zaman kanta ta tabbatar da labarin. Tun dai daga watan Oktoba na shekarar 2017 zaman lafiya a yankin mai magana da harshen Turancin Ingilishi da ke Kudu maso Yamma da makwaftansu na Arewa maso Yamma ke neman ya gagara sakamakon arangama tsakanin 'yan aware da jami'an tsaro, baya ga yawan yin garkuwa da mutane.