1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magudun adawa a Mali ya shiga hannun masu bindiga

March 26, 2020

Madugun adawa na kasar Mali Soumaila Cisse ya shiga hannun wasu masu garkuwa da mutane.

https://p.dw.com/p/3a67j
Porträt - Soumaila Cisse
Hoto: Getty Images/I. Sanogo

Mai magana da yawunsa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa an yi garkuwa da Cisse a wani yanki da ake kira Niafunke a daidai lokacin da suke tsakiyar yin gangamin yakin neman zaben 'yan majalisa da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi mai zuwa. 

Rahotanni sun ce ba wai magudun adawar kadai aka sace ba, akwai wasu jiga-jigan jam'iyyarsa da su ma 'yan bindiga suka tasa keyarsu zuwa wurin da kawo yanzu babu wanda ya san inda aka kaisu.

Kungiyar al-Qaida mai yaki da hukumomi ba ta dauki alhakin wannan aiki ba. Sai dai  wurin da lamarin ya faru wuri ne da kungiyar take da karfi a kasar Mali. Hukumomin kasar sun ce sun fara aiki tukuru wurin ganin an kwato jagoran 'yan adawar da kuma mukarrabansa da yanzu haka ke hannun yan bindiga.