1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi ganawa tsakanin Annan da Shugaba Assad

May 28, 2012

Kofi Annan ya yi kira ga shugabannin Siriya da su kawo karshen rikicin da ke wakana a kasar

https://p.dw.com/p/153eV
epa03239382 International envoy Kofi Annan speaks during a press conference upon arrival at the Dama Rose Hotel in Damascus, Syria on 28 May 2012. Annan arrived in Syria on 28 May 2012 for talks with Syrian officials on ways to end ongoing fighting in the country. "He is now in the hotel where the observers are staying," a source said. He is expected to meet Syrian President Bashar al-Assad on 29 May. EPA/YOUSSEF BADAWI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Kofi AnnanHoto: picture-alliance/dpa

Manzon kasa da kasa na musamman a Siriya, Kofi Annan ya gana da Shugaba Bashar Al Assad inda ya yi kira ga shugabannin wannan kasa da su ba da shedar da ke nuni da niyarsu ta samun bakin zaren warware rikicin kasar a cikin limana. Annan ya ce yana bukatar ganin shugaban Assad ya nuna karfin zuciya. Manzon na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) dai ya nuna bacin ransa game da kisan kiyashi da aka yi wa mutane asama da 100 mafi yawansu yara kanana a garin Hula. Kasar Rasha wadda da farko ta nuna adawa da matakan ake son daka akan Siriya ta hade da sauran mambobin komintin sulhu na MDD wajen yin Allah wadai da wadannan kashe-kashen. Su dai kasashen yamma da na Larabawa sun dora alhakin wannan kisa akan Assad. A dayan hannun Rasha da dora alhakin hakan akan gwamnati da kuma 'yan adawa ga baki dayansu.

A wani taron manema labaru na hadin-gwiwa tsakaninsa da takwaransa na Birtaniya, Willilam Hague ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya yi kira da a mai da hankali ga kawo karshen wannan rikici .Ya ce kasar ta Siriya kanta na bukatar daukar makomarta a hannun ta ba tare da tsoma bakin wata kasa ta ketare ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman