An yanke wa Hasan hukuncin kisa | Labarai | DW | 29.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yanke wa Hasan hukuncin kisa

Nidal Hasan, sojan Amirkan nan da ya aikata kisan dauki dai-dai a wani sansanin soji da ke garin Fort Hood na jihar Texas an yanke masa hukuncin kisa

Hasan mai shekaru 42 wadanda aka gayyata domin sauraron shari'arsa ne suka yanke masa wannan hukunci bayan da suka shafe sa'o'i hudu suna tafka muhawara akan hukuncin da ya fi dacewa da shi. Idan ba a manta ba a shekarar 2009 ne wannan mutun ya hallaka mutane 13 ya kuma raunata wasu 32 a jihar Texas. A ranar Jumm'ar da ta gabata ne dai ya amsa laifukan 45 da ake zarginshi da aikatawa. Hasan mai rike da fasfon din Amirka, mai asali daga yankin Palisdinu ya ce ya kashe abokan aikinsa ne saboda yakin da suka yi da Musulmai a Afganistan ba akan ka'ida ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu