An yanke hukuncin kisa ga masu fyade a India | Labarai | DW | 13.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yanke hukuncin kisa ga masu fyade a India

Kotu a Indiya ta ce mazan nan hudu da suka yi wa wata mata fyade a karshen shekarar da ta gabata za su fuskanci hukucin kisa bayan da aka same su da laifi.

Wata kotu a Indiya ta yanke hukuncin kisa ga mazan nan hudu da ake zargi da yi wa wata mata fyade a cikin shekarar da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta sakamakon raunuka da ta samu.

Kotun dai karakshin jagoracin mai shari'a Yogesh Khanna ta ce ta samu Mukesh Singh da Vinay Sharma da Akshay Thakur da kuma Pawan Gupta da laifi a saboda haka ba ta da wani zabi da ya wuce yanke musu hukuncin kisa to sai dai wannan hukuci zai tabbata ne bayan babbar kotun kasar ta tabbatar da shi.

Jim kadan bayan kammala yanke hukuncin, lauya A.P. Singh wanda ya kare mutane hudun da suka aikata fyaden ya yi ta karaji daidai lokacin da alkali ke barin teburinsa, inda ya ke cewar hukuncin da ya yanke ba na gaskiya bane kuma karen tsaye ne ga tsarin shari'ar kasar.

Al'ummar Indiya da dama dai sun yi na'am da wannan hukunci da aka yanke.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman