An yaba da matakin da Rasha ta dauka a kan rikicin kasar Yemen | Labarai | DW | 15.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yaba da matakin da Rasha ta dauka a kan rikicin kasar Yemen

Halin ya kamata da Rasha ta nuna ya kai ga zartas da kudurin sanya wa 'yan tawayen Yemen takunkumin sayar musu da makamai.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinemier ya yi maraba da kudurin da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya zartas,, inda ya sanya takunkumin sayar wa 'yan tawayen Houthi a kasar Yemen makamai. Steinmeier ya fada wa wani taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da ke wakana a garin Lübeck na nan Jamus cewa wannan matakin ya samu ne saboda halin ya kamata da kasar Rasha ta nuna. Rasha dai ta yi rowar kuri'arta amma ba ta hau kujerar naki ba a lokacin kada kuri'ar amincewa da kudurin sanya wa 'yan Houthi takunkumi. A kan rikicin na Yemen Steinemier cewa ya yi.

"Bisa la'akari da halin da ake ciki a Yemen, za mu tattauna kan damarmakin da muke da su na kawo karshen wannan rikici, wanda ke kara yin muni yake kuma janyo asarar rayuka a kullum."

Taron zai kuma tattauna kan rikice-rikicen da ake fama da su a duniya baki daya da kuma batun kare muhalli da na sufurin jiragen ruwa.