1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An wanke wadanda ake zargi a hatsarin Saudiyya

Abdul-raheem Hassan
October 1, 2017

Wata babbar kotu a Saudiyya ta wanke wasu mutane 13 da ake zargi da alhakkin rikitowar kugiya a masallacin birnin Makka, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mahajjata 110 a shekaru biyu da suka gabata.

https://p.dw.com/p/2l4B2
Golf Gipfel Saudi Arabien König Abdul Aziz
Hoto: picture alliance/Saudi Royal Council

Kotun ta kuma wanke kamfanin Binladen da ke da alhakkin tsarin ginin masallacin daga tushe, kotun dai ta ce hukuncin ya wanke mjtanen ne sakamakon rashin gabatar da kwararan hujjuji aka laifin da ake thumar su da aikatawa. To sai dai kotun ta ce akwai damar daukaka wannan kara.

A tun farko dai an zargi mutanen ne da yin sakaci da kuma ka'idojin kula da lafiyar al'umma, amma a baya kotun ta ce ba ta da hurumin zartar da hukunci a kan laifin da ake tuhumar mutanen sanadiyar faduwar kugiya a kan masallata a cikin masallacin birnin Makka.