An wanke Najeriya daga cutar Ebola | Labarai | DW | 20.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An wanke Najeriya daga cutar Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce Najeriya ta fita daga cikin kasashen da ke fuskantar barazanar Ebola

A wannan Litinin Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar da cewa an samu nasarar kawar da cutar Ebola daga Tarayyar Najeriya. Kwanaki 42 ke nan aka kwashe ba tare da samun wani sabon kamuwa daga cutar ba, adadin da ya nunka kwanaki 21 da cutar ta Ebola take bulla a jikin wanda ta kama.

A watan Yuli aka samu barkewar cutar bayan wani dan kasar Laberiya ya isa Najeriya ta jirgin sama. Tun kafin wannan lokacin Shugaban kasar ta Najeriya Goodluck Jonathan ya ayyana cewa kasar ta samu nasarar kawar da Ebola. Kafin kawar da ita ta hallaka mutane 8 a kasar daga cikin 20 da ta kama.

Sai dai cutar tana ci gaba da ta'adi a kasashen Gini, da Saliyo, da kuma Laberiya da ke yankin yammacin Afirka. Kawo wannan lokaci Ebola ta yi sanadiyar hallaka fiye da mutane 4500 yayin da ta kama fiye da mutane 9000.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe