1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tuhumi wani jigo cikin 'yan adawar kasar Kenya

Zulaiha Abubakar
February 6, 2018

Kotu ta tuhumi Miguna Miguna jigo daga cikin 'yan adawa a kasar Kenya da cin amanar kasa bayan samun sa da hannu cikin rantsar da madugun 'yan adawar kasar Raila Odinga a matsayin shugaban mutanen Kenya.

https://p.dw.com/p/2sC7d
Kenia symbolische Vereidigung Raila Odinga
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/B. Jaybee

Jami'an 'yan sanda sun gabatar da takardar sammaci da ga wata kotun yanki da ke Kajiado a kasar ta kenya, inda ake tuhumar  Miguna Miguna da shiga gaba lokacin wani gangami ba bisa ka'ida ba tare da cin amanar kasa ta hanyar rantsar da Raila Odinga  domin kama aiki a matsayin sabon shugaban mutanen kasar Kenya.

Zuwa yanzu dai gidajen talabijin masu zaman kansu a kasar sun sanar da cewar Miguna ya ki amsa laufukan da aka tuhume shi da su, jami'an tsaro sun kame shi a ranar Juma'a da ta gabata yayin da suka kai wani samame gidansa an kuma bayar da belinsa a kan kudi shilling dubu hamsin na kasar Kenya duk kuwa da cewar har yanzu yana hannun 'yan sanda.