An tuhumi shugabannin ′yan farar hula a Nijar | Labarai | DW | 11.07.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tuhumi shugabannin 'yan farar hula a Nijar

Wata kotu a matakin farko a Jamhuriyar Nijar ta tuhumi jiga-jigan kungiyoyin farar hula da laifin aikata zanga-zangar da hukumomin kasar suka haramta tare da zarginsu da haddasa dimbin hasara ga kadarorin gwamnati.

Niger Niamey Opposition (DW/M. Kanta)

Aliyu Idrissa a tsakiya da Nouhou Arzika a hagu lokacin wani gangami

An shafe tsawon sa'o'i 15 ana sauraren shari'ar da ta hada gwamnati da 'yan farar hula har izuwa tsakiyar daren Talata wanda daga karshe lauyan gwamnati ya ba da shawarar hukuncin daurin shekaru daga daya zuwa uku da ma tarar kudi jaka 100 na sefa ga 'yan fafatukar nan Malam Nouhou Arzika da Moussa Tchangari da Ali Idrissa. An kuma ayyana ranar 24 ga watan nan a matsayin ranar da za a ba da sakamakon karshe na shari'ar.

Tun a ranar 25 ga watan Maris hukumomin kasar suka cafke 'yan fafatukar da suka kira wani taron gangami da jerin gwano na lumana da zummar nuna adawa da dokar nan ta kasafin kudin kasar na wannan shekara da ke cike da cece-kuce bisa zargin cewar 'yan kungiyoyin sun shirya zanga-zangar ne bayan hukumomi sun haramta.

Akalla mutum 24 ne galibinsu 'yan farar hula da ke adawa da dokar kasafin kudin kasar ke hannun hukuma garkame a gidajen kaso ba tare da shari'a ba.