An tuhumi Janar Diendere da hannu a kisan Thomas Sankara | Labarai | DW | 07.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tuhumi Janar Diendere da hannu a kisan Thomas Sankara

Hukumomin Burkina Faso sun samu hannun babban sojan a dalilan da suka jawo kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara a shekarar 1987.

Burkina Faso Ouagadougou General Gilbert Diendere

Janar Gilbert Diendere

Mahukunta a Burkina Faso sun tuhumi Janar din sojan da ya jagoranci juyin mulki da ya gaza nasara a watan Satumba na wannan shekara da hannu cikin dalilan da suka jawo kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara a shekarar 1987.

Janar Gilbert Diendere wanda tun a yanzu ake tuhumarsa da laifin kitsa juyin mulki a kasar kuma tuhume shi da hannu a kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaba Thomas Sankara kamar yadda kotun da ke sauraren karar ta bayyana a ranar Lahadi, akwai wasu mutane goma da ake zargi da hannu kan wannan ta'asa wadanda duk suka kasance sojoji na musamman da ke ba da kariya ga fadar tsohon shugaba Blaise Compaore.