An tsinci gawawakin mutane 15 kusa da mahaƙar Gaz a Aljeriya | Labarai | DW | 19.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsinci gawawakin mutane 15 kusa da mahaƙar Gaz a Aljeriya

Dakarun Aljeriya da na ƙungiyar AQMI na ci gaba da fafatawa a mahaƙar Gaz ta In Amenas

Rahotani daga ƙasar Aljeriya sun bayana cewar aƙalla gawarwakin mutane 15 ne aka gani a kusa ga kamfanin Gaz na Tiguentourine a kusa ga inda aka yi garkuwa da 'yan ƙasashen waje. To saidai kamfanin dillancin labaran Reuteurs da ya bayana labarin,ya ce har ya zuwa yanzu ba a gano ko su wanene ba mutanen da aka ƙone,yayin da ministan tsaron ƙasar Faransa Jean Yves Le Drian ya ce bisa ga bayanan da suke da su, babu wani bafaranshe da ake ci-gaba da garkuwa da shi a ƙasar. Ko a yau, an yi ɓarin wuta tsakanin dakarun ƙundumbalar Aljeriya da mayaƙan Aqmi da ke ci gaba da tsare wasu mutanen da suka kai kimanin 20. An ma bayana cewar daga cikin masu garkuwa da mutanen har da wani dan Jamhuriyar Nijer mai suna Abdul Rahaman al Nigeri da ke matsayin mataimakin jagoran ƙungiyar ta Alqa'ida a Magrehb wato Mokhtar Belmokhtar.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadisou Madobi