An tsawaita belin Oscar Pistorius | Labarai | DW | 12.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsawaita belin Oscar Pistorius

Kotun Afirka ta Kudu za ta yanke wa Pistorius hukunci a watan gobe na Oktoba

Kotun kasar Afirka ta Kudu ta tsawaita belin da ta bai wa mashahurun dan tseren kasar mai kafafun roba, Oscar Pistorius zuwa ranar 13 ga watan gobe na Oktoba, lokacin da za a karanta hukuncin da aka yanke masa, bayan da aka same shi da laifin kisa ba da gangan ba.

Mai shariya Thokozile Masipa ta wanke Pistorius bisa sauran manyan laifuka da aka zarge shi. Amma duk da haka zai iya shafe shekaru 15 a gidan fursuna mafi yawa, sai dai ya danganta da abin da mai shariyar ta bayyana. A shekarar da ta gabata ta 2013 Pistorius ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp, lamarin da ya dauki hankalin al'umar kasar ta Afirka ta Kudu da kafofin yada labarai na duniya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman