1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaurara tsaro a Indiya

April 10, 2019

Yayin da ake haramar zabe a Indiya, an soma daukar matakan ganin komai ya tafi ba tare da samun wata rigima ba. Akwai dai bangarorin kasar da ke fama da rigingimu.

https://p.dw.com/p/3GYtx
Indien Konflikt um Zugang von Frauen zu Sabarimala-Tempel
Hoto: Getty Images/AFP

Hukumomi a kasar sun baza dubban jami'an sanda da sauran wasu masu kayan sarki a sassan jihohi 29 da wasu cibiyoyi biyu na tarayya, gabanin zaben 'yan majalisar dokoki.

A mazabu 91 ne za a fara zaben a tashin farko a ranar Alhamis, zaben kuma da za a yi a matakai bakwai daban-daban, a kuma kammala ranar 19 ga watan gobe na Mayu.

An dai tsananta matakan tsaro a yankunan Jammu da kuma jihar Kashmir, wadanda duk ke fama da fitintinu.

Akwai wasu rahotanni da ke cewa dakaru za su yi sintiri na musamman, a dukkanin wuraren da ke kan hadarin fuskantar barazana lokacin zaben.