An tsare bakin hauren Afirka da ke fatan shigowa Turai a Libya | Labarai | DW | 08.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsare bakin hauren Afirka da ke fatan shigowa Turai a Libya

A kullum daruruwan 'yan Afirka musamman daga kasashen Kudu da Sahara ke kokarin gwada sa'arsu ta shigowa Turai daga Libya.

Jami'an tsaron kasar Libya sun tsare bakin haure kusan 300 daga kasashen Afirka Kudu da Sahara, wadanda suka boya a wata gona a birnin Tripoli suna jiran wani jirgin ruwa da zai kawo su Turai. Abdel Nasser Hazem shi ne kakakin ma'aikatar yaki da bakin haure a Libya wanda ya yi karin haske.

"Ofishin bincike na birnin Tripoli ya kai samame a wani sansanin bakin haure da ke birnin. Akwai mutane kimanin 289 daga kasashe daban-daban. An kama su kuma an kawo su nan wurin, yanzu haka kuma mun fara shirye-shiryen mayar da su kasashensu na asali."

A kowace shekara dai dubun dubatan 'yan Afirka Kudu da Sahara na bi ta Libya a kokarinsu na neman shigowa nahiyar Turai ta tekun Bahar Rum.