1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Gabatar da jadawalin zaben 'yan majalisa

Gazali Abdou Tasawa
July 2, 2020

Hukumar zaben kasar Chadi ta fitar da sabon jadawalin zaben 'yan majalisar dokokin kasar wanda ta ce za a gudanar da shi a ranar 21 ga watan Oktoban shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/3eiSX
Tschad | Kodi Mahamat - Vorsitzender der Unabhängigen Nationalen Wahlkommission
Hoto: DW/B. Dariustone

Gidan radioyn kasar ta Chadi ne ya sanar da hakan a wannan Alhamis, inda ya ce shugaban hukumar zaben kasar ta Chadi Kodi Mahmat Bam ya kuma ya jaddada ranar zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Aprilun shekarar ta 2021 wato watanni shida kafin zaben 'yan majalisar.

 A baya dai Sau biyar a baya Shugaba Idriss Deby na dage zaben 'yan majalisar a bisa hujjar matsalolin tsaro da na tattalin arziki da kuma na annobar Corona a baya bayan nan.

 Shugaba Idriss Deby wanda ke kan karagar mulkin kasar ta Chadi bayan wani juyin mulki da ya yi a shekara ta 1990, zai sake tsayawa takara a zaben na 2021 a wani sabon wa'adin shekaru biyar.