An tsagaita wuta a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 11.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

An fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Sudan ta Kudu bayan bangorirn da ke rikici da juna sun yi alkawarin yin haka

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce an fara aiki da yarjejeyar tsagaita wuta wadda ta kawo karshen yakin basasan kasar na watanni biyar.

Ranar Jumma'a Shugaba Salva Kiir da madugun 'yan tawaye kuma tsohon mataimakin Shugaban kasa Riek Machar suka rantaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, yadda ta tanadi tsagaita wuta cikin sa'o'i 24. Kasashen duniya da suka saka kaimi wa bangarorin sun yi maraba da yarjejeyar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu