An tarwatsa ′yan Biafra a Port Harcourt | Labarai | DW | 10.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tarwatsa 'yan Biafra a Port Harcourt

'Yan Awaren na Biafra sun gudanar da zanga-zanga a birnin Port Harcout don tilasta wa hukumomi sako wani mambansu. Amma kuma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da harsasan roba da kuma hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa zanga-zangar da masu rajin kafa kasar Biafra suka gudanar a birnin Port Harcourt da ke yankin Kudu maso gabashin Najeriya. Suna nema a sako wani dan aware mai suna Nnamdi Kanu da aka kame tun watan Kktoba sakamakon watsa shirye-shiryen a wata rediyo da suka kafa ba bisa ka'ida ba.

Wasu da suka shaidar da gangami na Biaffra sun bayyana cewar jirage masu saukar angulu sun yi shawaki a sararin samaniyar birnin Port harcourt. sai da kuma kwamishinan 'yan sandan wannan jiha ta Rivers ya karyata rade-raden da ake yayatawa cewa sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa 'ya awaren na Biafra.

Irin wannan yunkuri na neman ballewa daga Najeriya ya taba haddasa yakin basasa a baya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane miliyan daya.