An tarwatsa masu zanga-zanga a Mali | Labarai | DW | 27.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tarwatsa masu zanga-zanga a Mali

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya sun tarwatsa yunkurin kai hari a ofishin su dake Mali

Rahotanni daga kasar Mali, sun ce sojojin kiyaye zaman lafiya na MajalisarDinkin Duniya, sun tarwatsa wani gungun masu zanga-zanga a arewacin kasar, wadanda suka doshi ofishin majalisar dake yankin.

Shaidu sun ce sojojin sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan dubun dubatan masu zanga-zanga, inda akalla mutun guda ya rasa ransa, sakamakon harbi da bindiga da jami'an suka yi.

Wani mai magana da yawun ofishin na Majalisar Dinkin Duniya, Oliver Salgado bai tabbatar da zargin da aka yi kan sojin da amfani da harsashin gaske kan mutumin da ya mutun ba, yana mai cewa an dai yi amfani ne da hayakin wajen tarwatsa masu zanga-zangar, wadanda a cewar sa suka yi ta jifar ofishin da duwatsu a kokarin su na kutsawa ciki.