An tarwatsa masu zanga-zanga a Gezi Park | Labarai | DW | 08.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tarwatsa masu zanga-zanga a Gezi Park

'Yan sandan Turkiya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu bore a birnin Santambul awowi kalilan bayan an sanar da sake bude wurin shakatawa na Gezi Park.

'Yan sandan kwantar da tarzoma a Turkiya sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla, da feshin ruwa, da kuma harsasan roba don hana masu zanga-zanga shiga wurin shakatawa na birnin Santambul, wurin da ya haifar da mummunar tashin-tashina da ta addabi kasar a watan da ya gabata. Matakin 'yan sandan ya biyo bayan sake bude wurin shakatawa na Gezi Park ga jama'a da hukumomi suka yi a wannan Litinin. Da farko dai gwamnan birnin Santambzul Huseyin Avni Mutlu ya ba da sanarwar sake bude Gezi Park makonni uku bayan da 'yan sandan kwantar da tarzoma sun fatattaki masu zanga-zanga a wani mataki na kawo karshen boren adawa da shirin gwamnati an sake fasalin wuri shakatawar. Sai dai awowi kalilan 'yan sanda sun sake rufe Gezi Park din bayan da masu zanga-zangar kyamar gwamnatin Firaminista Recep Tayip Erdogan sun kira da a gudanar da wani gangami da yammacin wannan Litinin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh