An tabbatar da mutuwar daliban Mexiko | Labarai | DW | 28.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tabbatar da mutuwar daliban Mexiko

Gwamnatin kasar Mexiko ta tabbatar da mutuwar daukacin dalibai 43 da suka bata tun watan Satumba na shekara ta 2014

Babban mai shigar da kara na kasar Mexiko Jesus Murillo ya ce babu tantama daukacin daliban kasar 43 da suka bace tun watan Satumban da ya gabata sun mutu. Ya ce an yi kuskuren zaton cewa daliban suna cikin wani bangaren gungun masu aikata laifuka.

An soki yadda gwamnatin kasar ta tunkari lamarin bacewar daliban, yayin da iyalai ke cewa wannan bayani bai gamsar ba. Dubban 'yan kasar ta Mexiko sun yi gangami tir da bacewar daliban, inda suke neman ganin an nemo daliban a mace ko a raye. Lamarin ya bata sunan gwamnatin Shugaba Enrique Pena Nieto.