An soma tattauna rikicin Burundi | Labarai | DW | 23.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soma tattauna rikicin Burundi

Majalisar Ɗinkin Duniya na shiga tsakanin a rikicin siyasar da ake yi a ƙasar.

Manzon musammun na Majalisar ta Ɗinkin Duniya a yankin Afirka ka Tsakiya Abdoulaye Bathily ya jagoranci wata tattaunwa,tsakanin 'yan siyasar haɗe da wakilai na ƙungiyoyin fara hula da na addinai,sai dai wakilan jam'iyyar da ke yin mulki ba su hallarci ganawar ba,

Nan gaba ne a ƙarshen wannan wata za a yi zaɓen 'yan majalisun dokoki da na ƙananan hukumomin a Burundi,wanda ke ciki da rikici kafin zaɓen shugaban ƙasar wanda shugaba Pierre Nkurunziza ya dage ga yin takara ta uku duk kuwa da ƙin amincewar 'yan adawar