An soma sulhunta rikicin mulki a Kano | Labarai | DW | 08.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soma sulhunta rikicin mulki a Kano

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, an kama hanyar warware takaddamar da ta tasamma janyo hargitsi sakamakon takun saka tsakanin gwamnati da kuma masarauta.

A ranar Juma'a ne aka sami labarin Shugaban Najeriya Muhammad Buhari tare da kungiyar gwamnonin kasar tare da attajirin nan na Afirka Alhaji Aliko Dangote, suka sa baki tare da zaman sulhu domin kawo karshen tsamin dangantaka tsakanin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin Kano Muhammad Sunusi na biyu.

Rikicin siyasa ce ta sa gwamnatin Kanon daukar matakin kirkirar sabbin masarautu 4 tare kuma da binciken sarkin kan zargin almubazzaranci da kudin masarautar.

Mashawarcin gwamnan Kano a fannin yada labarai da kafar sadarwa Salihu Tanko Yakasai  wanda ke Abuja inda ake zaman sulhun, ya ce an cimma sulhu amma batun sabbin masarautu na nan.