An soma gudanar da zabe a Afghanistan a cikin tsoro | Labarai | DW | 05.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soma gudanar da zabe a Afghanistan a cikin tsoro

A wannan Asabar 'yan kasar Afghanistan ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa zagaye na farko mai cike da fargaba da kuma yanayi na rashin sanin tabbas.

Tun dai da musalin karfe bakwai ne agogon kasar, karfe biyu da rabi ke nan agogon GMT, aka buda runfunan zabe, yayin da Shugaba Hamid Karzai mai barin gado ya kada kuri'arsa tare da yin kira ga 'yan kasar da su fito domin kada kuri'unsu ba tare da jin tsoro ba.

Shugaba Karzai yace a yau muna cikin rana mai tarin muhimmanci dangane da makomarmu, da kuma makomar kasarmu baki daya, don haka ina kira ga dukkan al'ummar wannan kasa, da suje runfunan zabe domin sauke nauyin da ya rataya a kansu, duk da cewa ana ruwan sama, ga kuma sanyi, da ma barazanar abokan gaba, domin mu bai wa wannan kasa damar samun wata sabuwar alkibla.

Kalubale uku ne dai ke fuskantar wannan zabe na kasar Afghanistan, da suka hada da barazanar 'yan Taliban, da tsammanin magudi, sannan da kuma yiyuwar samun karancin masu fitowa kada kuri'ar, sakamakon alwashin da 'yan Taliban suka sha na kai hare-hare a ranar zaben.

'Yan takara guda takwas ne dai ke fafatawa a wannan zabe, kuma an baza sojoji fiye da dubu 350 domin kare lafiyar masu zabe a wannan kasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal