An soma gudanar da yaƙin neman zaɓen ƙananan hukumomi a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 06.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soma gudanar da yaƙin neman zaɓen ƙananan hukumomi a Cote d'Ivoire

Za gudanar da zaɓuɓɓukan ranar 21 ga watan Afrilu, a wani mataki na daddale tafarkin Dimokradiyyar da ƙasar ta kama hanyar aiwatar wa shekaru biyu da suka wuce.

An Ivorian woman casts her ballot in presidential elections in Abidjan, Ivory Coast, 31 October 2010. Voters turned out in their numbers to cast their ballots in the historic elections, the first time in 10 years following years of delays and political intsability. EPA/NIC BOTHMA

Babbar jam'iyyar adawa ta tsohon shugaban ƙasa wato Laurent Gbagbo na ƙaurace wa zaɓen. Masu lura da al'amura na ganin wannan shawara da jam'iyyar ta FPI ta yanke na yin ƙafar ungulu ga zaɓen.

Ko a zaɓen ' yan majalisun dokoki na shekara ta 2011 da aka gudanar FPI ta hau kujerar naƙi, na zaman wani mataki na rushe shirin tattaunawa da sake sasanta tsakanin al'ummar ƙasar da gwamnatin Alassane Ouattara ta ƙaddamar tun a watan Yuni da ya gabata. Yan takara sama da ɗari takwas ne zasu gogga a zaɓen a mataki daban daban kama daga zaɓen ƙananan hukumomin da kuma na jihohin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi