1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soki lamirin 'yan siyasa a Nijar saboda rashin jituwa

Abdoulaye Mamane Amadou/ MNASeptember 23, 2015

Kungiyoyin farar hula da masu rajin kare demokradiyya sun yi tir da tabi'un 'yan siyasa na gaza magance rikicin siyasa a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/1GbqL
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Babban zaman taron majalisar ta tattauna al'amuran siyasar kasar Nijar wato CNDP da aka jima ana jiran ganin kiransa daga bangaren gwamnati, na daga cikin wasu mahimman hanyoyin da al'umma da ma wasu kungiyoyin fararen hula suka yi ta kyakyawan fata a kansa, domin ganin an cimma bakin zaren warware kullin wata bakar fitina da bakin rikicin siyasar kasar da yakan kama a tsakanin 'yan adawar da na masu rinjaye.

Sai dai duk da wannan fatan wani abin da jama'a da dama ba su taba sa tsammani ba shi ne taron ya tashi baram-baram ba tare da cimma wata masalaha ba tun daga farkonsa kan ajandar da taron zai tattauna a kai kafin ma bangarorin biyu su shiga cikin mahawarar gadan gadan. Abubuwan da suka kara harzuka wasu al'umma da ma kungiyoyin fararen hular da suka jima suna mafarkin ganin an shirya tsakanin 'yan adawa da bangaren masu rinjaye.

Rashin jin dadi da halayyar 'yan siyasa

Malam Siradji Issa na kungiyoyin Mojen na daga cikin 'yan kungiyoyin fararen hular da suka ce sun yi Allah wadarai da abinda 'yan siyasar suka nuna wa al'umma a ranar Talata.

"Mu muna cikin wadanda suka tilasta wa gwamnati da cewar dole su kira wannan ranar saboda ganin halin da aka shiga. Wannan hanyar ce kawai za a iya a samu mafita saboda matsaloli ne da a fannin siyasa kawai ake iya gyarasu. Rashin cimma daidaito yana nuna rashin kishin kasa da 'yan siyasa suka nuna kuma yana nuna cewar sun nuna son kai da son rai, domin a zamantakewar 'yan siyasar ma ba a jituwa saboda hakan dole sai an samu mafita, dole sai an tattauna, dole sai an shirya zabe."

Niger Niamey Opposition
Jerin gwanon 'yan adawa a birnin YamaiHoto: DW/M. Kanta

Sai dai a yayinda 'yan adawa da bangaren masu rinjayen ke fuskantar matsanancin ra'ayi, haka abin yake hatta ma a bangaren wasu kungiyoyin fararen hular da ke fafatukar kare demokradiyya. Wasu 'yan kungiyoyin dai ire-iren Malam Nassirou Saidou na Muryar Talaka na mai ganin cewar duk wata magana kan jadawalin zabe da 'yan adawar ke son hukumar ta CNDP ta maido a kan teburin tattaunawa a barta.

"Mu mun yarda dangance da matsalolin da suke ciki na cece-kuce a kirayi wannan dakin na shawara domin su tsaya su tattauna a kan abubuwan da suka shafi siyasa. Su warwaresu domin mu tinkari zabe. To amma ba za mu amincewa ba da a komo baya game da abinda CENI ta fadi kamar yadda su 'yan adawa suke so. Wai har a koma baya ko kuwa a cewa CENI wani abu ba mu yarda ba."

Sake kiran sabon taro don samun mafita

Kungiyoyin fararen hular dai sun ce za su bi sau da kafa domin tilasta wa hukumomin kolin kasar sake kiran wani babban taro na majalisar domin halin da ake ciki yanzu na nuna cewar Nijar na kan hanyar shiga wani yanayi mai alamun rashin tabbas.

"Dole adawa ta yi baya da wasu abubuwa, su kuma majoriti idan harma 'yan adawa na son wata fitina to su bullo da wasu hanyoyi da za su hana fitina. Saboda hakan a kara kiran wani taro don a samu sasantawa. Dole ne a kira taron nan dole ne a cikin gagawa a tsaida maudu'in da kowa zai amincewa da shi a zauna a tattauna saboda a samu mafita."


Yanzu haka dai hankalin jama'a ya karkata a kan batun ranar da za a sake kiran wani babban taro bayan hayaniyar da aka samu a ranar Talata ta haifar da dage taron. Hukumar dai ta sha warware matsalolin siyasa da dama wadanda suka shafi tafiyar demokradiyyar Nijar duk da rashin jituwar da ake samu a tsakanin gungun jam'iyyu sama da 80 da ke da wakilci a majalisar.