An soki lamirin Jamus dangane da ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 24.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soki lamirin Jamus dangane da 'yan gudun hijira

Gwamnatin Ostriya ta ce dole ne a hada karfi don tinkarar matsalar kwararowar 'yan gudun hijirar zuwa kasashen yammacin Turai.

Ministan harkokin wajen kasar Ostriya Sebastian Kurz ya sake sukar manufofin Jamus kan 'yan gudun hijira. Ministan ya ce dole ne a hada karfi don rage yawan kwararowar 'yan gudun hijirar, inda ya kara da cewa a shirye gwamnatin birnin Vienna take ta hada kai da takwararta ta Berlin, a saboda haka suna sa ran cewa Jamus za ta fada musu ko a shirye take ta dauki karin 'yan gudun hijira da kuma yawansu. A wannan Laraba ce gwamnatin Ostriya ke karbar bakwacin taron ministocin cikin gida da na harkokin wajen kasashen da ke yamma da yankin Balkan, inda za su tattauna kan rage kwararar 'yan gudun hijira ta wannan hanya. Ministan harkokin wajen na Ostriya Sebastian Kurz ya kuma soki lamirin mahukuntan kasar Girka yana mai cewa.

"A taron da muka yi a birnin Amsterdam makonni uku da suka wuce na gano cewa Girka ba ta da niyya ta rage yawan kwararowar 'yan gudun hijira. Maimakon haka tana jigilarsu ne zuwa tsakiyar Turai. Wannan abu na ci mana tuwo a kwarya."