An soki hukuncin kisa da aka yanke wa tsaffin jami′an Libiya | Labarai | DW | 28.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soki hukuncin kisa da aka yanke wa tsaffin jami'an Libiya

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna takaici hanyoyin da aka bi wajen yanke hukuncin kisa wa dan Marigayi Shugaba Mu'ammar Gaddafi na Libiya

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin dan Adam ta nuna damuwa kan hukuncin kisa da aka yanke wa Saif al-Islam dan-Marigayi Mu'ammar Gaddafi tsohon shugaban kasar Libiya. Hukumar ta ce matakan shari'ar da aka bi sun gaza cika mizanin kasashen duniya.

A wannan Talata wata kotun kasar ta Libiya ta yanke hukuncin kisa ga Saif al-Islam da wasu jami'ai takwas na tsahuwar gwamnatin Marigayi Gaddafi, wadda aka kawo karshen gwamnati sakamakon juyin-juya halin shekara ta 2011. Tun wannan lokaci kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka mai arzikin man fetur ta fada cikin rudanin siyasa da tattalin arziki.